Kotu ta zargi Donald Trump da yin amfani kudaden gidauniya don siyasa
An shigar da kara a gaban kotu inda ake zargin shugaban Amurka Donald Trump da kuma ‘yayansa biyu da yin amfani da kudaden wata gidauniya mallakin shugaban domin gudanar da yakin menan zabensa, abin da kuma ya saba wa ka’ida.
Wallafawa ranar:
Mai shigar da kara ta gwamnati a birnin New York Barbara Underwood ce ke zargin mutanen da yin amfani da kudaden gidauniyar don siyasa a shekarar 2016 maimakon ayyukan jinkai wadanda su ne manufofin kafa gidauniyar.
Tun bayan lashe zaben Amurka Shugaban kasar Donald Trump ke ci gaba da sa kafar wando da bangaren shara’ar kasar Amurka .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu