Isa ga babban shafi
Iran-nukiliya

Iran ta koma shirinta na inganta makamashin Uranium

Iran ta sanar da maido da aikinta na inganta makamashin Uranium, a matsayin madogararta, idan har yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da kasashen Turai ta rushe.Shugaban hukumar bunkasa makamashin nukiliya na Iran Ali Akbar Salehi, ya ce tuni gwamnatin kasar ta sanar da majalisar dinkin duniya matakin nata, cikin wasikar da ta aikemata.

Matakin dai na da nufin Idan har kasashen Turai suka kammala ficewa daga yarjejeniyar ta 2015, kasar za ta samu bangaren da za ta rike don dogaro da kai tare da zame mata babbar kariya daga irin illar da takunkuman za su yi mata.
Matakin dai na da nufin Idan har kasashen Turai suka kammala ficewa daga yarjejeniyar ta 2015, kasar za ta samu bangaren da za ta rike don dogaro da kai tare da zame mata babbar kariya daga irin illar da takunkuman za su yi mata. REUTERS/Stringer/Files
Talla

Matakin na Iran dai ya biyo bayan janyewar da Amurka ta yi daga yarjejeniyar nukiliyarta, a watan da ya gabata.

Yarjejeniyar da aka cinmma a 2015, tsakanin kasar ta Iran da Faransa, Amurka, Jamus, Birtaniya, Rasha da kuma China, ta bukaci Iran ta rage matakin inganta makamashin Uranium zuwa kashi 3 a maimakon aikin inganta makamashin da ta ke yi kan matakin kashi 90, abinda zai bata damar mallakar makaman nukiliya cikin sauri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.