Isa ga babban shafi
Duniya

Taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G7

Faransa ta bukaci Amurka ta baiwa kasashen Turai da kawayen ta dake cikin kasashen da suka fi karfin tattalin arziki na duniya da ake kira G7 tabbaci mai kyau domin kaucewa rikicin kasuwanci.

Taron kasashe masu karfin tattalin arziki a Duniya,G7
Taron kasashe masu karfin tattalin arziki a Duniya,G7 REUTERS/Ben Nelms
Talla

Ministan kudin Faransa Bruno Le Maire ya bayyana haka wajen taron kungiyar G7 da aka yi a Canada, inda yake cewa yanzu kallo ya koma wurin Amurka na sake fasalin tafiyar ta, ko kuma ta fuskanci matsala.

Le Maire yace Amurka na da yan kwanaki kadan ne domin sauya matsayin da ta dauka na kakabawa Turai da Canada da Mexico haraji ko kuma ta gamu da fushin kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.