Isa ga babban shafi
Amurka-Korea

Trump ya tabbatar da zuwan jami'an Korea ta Arewa New York

Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da cewar manyan jami’an kasar Korea ta Arewa na kan hanyarsu ta zuwa Amurka, a wani bangare na shirye-shiryen ganawar shugabannin kasashen biyu da aka shirya gudanarwa ranar 12 ga watan Yuni a Singapore.

Kasashen biyu masu gaba da juna a baya sun amince da tattaunawa da junansu ne bayan shiga tsakanin da Korea ta kudu ta yi wadda ke matsayin kawa ga Amurka.
Kasashen biyu masu gaba da juna a baya sun amince da tattaunawa da junansu ne bayan shiga tsakanin da Korea ta kudu ta yi wadda ke matsayin kawa ga Amurka. Fuente: Reuters.
Talla

Tattaunawar kasashen biyu masu gaba da juna, an jima ana yayata batun ta wadda ke da nufin kawo karshen kera makaman kare dangi na Nukiliya da Korea ta arewan ke yi dama barazanar da ta ke ga Amurka.

Sai dai bayan kammala shigar kasashen da ke sasanta Amurkan da Korea ta Arewan daga bisani kasashen biyu sun yi tirjiya kan tattaunawar bayan tun da farko sun amince da ita, inda bangarorin biyu suka dan shiga yin dari-dari da juna, har ta kai shugaba Trump bayyana cewar ga alama haduwarsu da Kim ba za ta yiwu ba.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce a ganawar wakilan kasashen biyu yau a birnin New York, za ta samar da alkibla wadda shugabannin biyu za su dora tattaunawar ta su akai, kari ga batun samarwa juna cikakken aminci da zai tabbatar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.

Tawagar ta Korea ta Arewa dai na a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasar Kim Young Chol yayinda kawo yanzu ba a bayyana ainahin wadanda za su kasasnce a tawagar Amurka ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.