Isa ga babban shafi
Afrika-Korea

Afrika za ta samu tallafin Dala biliyan 5 daga Korea

Gwamnatin  Koriya ta Kudu ta sanar da tallafa wa kasashen Afrika da kudaden da suka kai Dala biliyan 5 ta hannun Bankin Raya kasashen Afrika domin bunkasa tattalin arzikinsu.

Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika Akinwumi Adesina da ya sanya hannu kan yarjejeniyar bada Dala biliyan 5 da Korea ta Kudu ta yi alkawari
Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika Akinwumi Adesina da ya sanya hannu kan yarjejeniyar bada Dala biliyan 5 da Korea ta Kudu ta yi alkawari ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Gwamnatin Korea ta Kudu ta bayyana shirin ne bayan tattaunawar da suka yi da wakilan Bankin Raya Kasashen Afrika na ADB da ya gudanar da taronsa na 53 a birnin Busan.

Taron wanda ya janyo ministocin kudi daga kasashen Afrika da masu zuba jari ya mayar da hankali ne kan shirin gina masana’antu da manyan ayyukan raya kasa da kuma bunkasa harkokin noma.

Gwamnatin Korea ta ce, za ta bada Dala biliyan 5 ne a cikin shekaru biyu masu zuwa ta hannun Bankin Raya kasashen Afrika da kuma wasu hukumomi na daban.

Shugaban Bankin Raya Afrika, Akinwumi Adeshina tare da mataimakin Firaministan Korea, Dong Yeon Kim sun sanya hannu kan yarjejeniyar bada tallafin.

Shi ma Bankin Korea ya sanya hannu kan wata yarjejeniyar bada Dala miliyan 600 domin bunkasa hanyar samar da wutar lantarki a Afrika.

Cikin manyan bakin da suka halarci taron har da Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na Biyu da ya kasance tsohon gwamnan babban bankin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.