Isa ga babban shafi

Mai yiwuwa a dage tattaunawar Amurka da Korea ta Arewa

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ana iya jinkirta ganawar da suka shirya yi da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un sabanin yadda aka shirya da farko, yayin da ya jaddada aniyar sa na ganin shugaban na Koriyar ya lalata makamin nukiliyar kasar.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Yayin da ya karbi shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in a fadar sa dake Washington, shugaba Donald Trump ya bayyana cewa akwai alamu dake nuna cewa ganawar da suka shirya yi ranar 12 ga watan gobe a Singapore da shugaba Kim Jong Un ba zata yiwu ba, sai dai zuwa wani lokaci nan gaba.

Trump dai yayi ta bayyana shirin ganawar a matsayin babbar nasara a gare shi, inda yake cewa a cikin shekara guda yayi abinda babu wani shugaban Amurka da yayi, wajen kubutar da Amurkawan da aka tsare, da kuma bude kofar tattaunawa da shugaban Koriyar da zummar lalata makaman sa.

Shugaba Trump ya baiwa kowa mamaki wajen shadawa duniya cewar shugaba Kim zai cigaba da zama a karagar mulki muddin ya lalata makaman sa, kana Amurka zata taimakawa kasar wajen sake gina tattalin arzikin ta.

A makon jiya ne Koriya ta Arewa ta sanar da barazanar kauracewa taron da kuma katse tuntubar juna tsakanin ta da Koriya ta kudu, a dai dai lokacin da ake ganin kamar an shawo kan kasar wajen watsi da shirin nukiliyar ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.