Isa ga babban shafi
Venezuela

Maduro ya lashe zaben Venezuela cikin rudani

An ayyana shugaban Venezuela, Nicolas Maduro a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da ‘yan adawa suka kauracewa saboda zargin rashin sahihancinsa.

Kasashen duniya sun yi tir da nasarar da Nicolas Maduro zai ya samu a zaben Venezuela saboda zargin rashin sahihancinsa
Kasashen duniya sun yi tir da nasarar da Nicolas Maduro zai ya samu a zaben Venezuela saboda zargin rashin sahihancinsa REUTERS/Carlos Garcia Rawlins
Talla

Kimanin kashi 46 na masu kada kuri’u ne suka fita rumfunan zaben shugabancin kasar a jiya Lahadi duk da cewa ‘yan adawa sun kaurace wa zaben, sannan kasashen duniya suka yi tir da shi.

Yanzu haka dai an ayyana shugaba Nicolas Maduro a matsayin wanda zai ci gaba da jagorancin kasar har zuwa nan da shekarar 2025.

Tun dai gabanin fitar da sakamakon zaben, babban mai adawa da Maduro, Henri Falcon ya shaida wa manema labarai cewa, ba su amince da tsaren-tsaren gudanar da zaben ba.

Mr. Falcon ya ce, babu wani zabe da aka gudanar a wurinsu, don haka ya zama tilas a shirya sabon zabe.

Tuni shugaba Maduro ya jinjina wa nasarar da ya samu ta sake shafe wa’adin shekaru 6 akan karagar mulki da ya bayyana a matsayin wani abu mai cike da tarihi.

Sakamakon zaben,ya nuna cewa, Maduro ya samu kashi 67. 7 cikin 100, yayin da Falcon ya samu kashi 21.2.

Sai dai wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar gabanin zaben na jiya, ta nuna cewa, ‘yan takarar biyu na kafa-da-kafa da juna wajen samun yawan kuri’u.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.