Isa ga babban shafi
Chile

Zargin lalata da yara ya tilastawa limaman Katolika 34 murabus

Akalla shugabannin mabiya darikar katolika 34 ne suka ajje aikinsu yau din nan bayan wani zargin lalata kananan yara da aka bankado wadda ta kai su ga tattaunawar kwanaki 3 da jagoran mabiya darikar ta Katolika na duniya Fafaroma Francis.

Jagoran mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis.
Jagoran mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis. REUTERS/Stefano Rellandini
Talla

Matakin ajje aikin na ialhirin limaman Katolikan 34 da ke fadin kasar ta Chile ya biyo bayan ganawar da suka yi da Fafaroma wanda ya bukaci da su yi hakan don nuna alhinin abun ga wadanda ya shafa.

Sanarwar da fadar Fafaroma ta Vatican ta fitar a yau, ta ce shugabannin 34 sun mika takaddar murabus dinsu ga jagoran darikar na duniya Fafaroma Francis wanda ya mika sakon neman yafiya ga daukacin mabiyansu da ke kasar ta Chile.

Tun farko dai Fafaroman ne ya yi sammacin jagororin su 34 bayan bankado zargin wanda a cewarsa ke matsayin babban tashin hankali ga jagorancinsa.

Dubban mabiya Katolika a kasar ta Chile na dora laifin kan jagororin majami'un kasar wadanda ke rufa-rufa tare da nuna halin ko'in kula kan zargin lalata da kananan yara da ake kan limamin Fernando karadima wanda lamarin ya yi tsnani tsakanin shekarun 1980 zuwa1990.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.