Isa ga babban shafi
Amurka-korea ta Arewa

Ana fuskantar koma baya a tattaunawar Amurka da Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta ce ba zata tattauna da makwabciyarta ta Kudu ba, a cikin yanayin koma bayan huldar diflomasiyya tsakaninsu, har sai ta janye daga atisayen sojin da ta shiga da Amurka a yankin na Korea tare da neman afuwarta.

Shugabanin kasashen Koriya ta Arewa da Amurka
Shugabanin kasashen Koriya ta Arewa da Amurka 路透社
Talla

A ranar Laraba 16 ga watan da ya gabata aka tsara ganawar wakilan kasashen biyu, amma da sanyin safiyar ranar Korea ta Arewa ta sanar da janyewa, a dalilin atisayen sojin hadin gwiwa tsakanin Korea ta Kudu da Amurka da suka soma a ranar 11 ga watan Mayu da muke ciki.

Hakan zai iya tuzura Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un janyewa daga batun ganawa da Shugaban Amurka Donald Trump a Singapore, sai dai shugaban na Amurka ya gargadi shugaban na Korea da cewa lalata tashoshin sarrafa nukiliyar kasar ne ya fi zama alheri mudin ba shi bukatar fuskantar matsaloli kamar yadda marigayi Kanal Ghadafi na Libya ya samu kan sa a lokacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.