Isa ga babban shafi
Amurka-Kamaru

Amurka na zargin kamaru da kisan fararen hula a yankin 'yan aware

Kasar Amurka ta zargi hukumomin Kamaru da amfani da tashin hankalin da ake samu a Yankin da ake amfani da Turancin ingilishi wajen kashe mutane da kuma cin zarafin jama’a.

Gargadin na Amurka na zuwa ne jim kadan bayan Jakada Peter Berlarin ya gana da shugaba Paul Biya a Yaounde.
Gargadin na Amurka na zuwa ne jim kadan bayan Jakada Peter Berlarin ya gana da shugaba Paul Biya a Yaounde. REUTERS/Joe Penney
Talla

Wata sanarwa da Jakadan Amurka a Kamaru, Peter Berlerin ya rabawa manema labarai ta nuna damuwar Amurkan kan halin da ake ciki a Yankin na 'yan aware mai amfani da turancin Ingilishi, ganin yadda jami’an tsaron Kamaru ke amfani da karfin da ya wuce kima wajen cin zarafin jama’a da kuma kashe su.

Jakadan ya ce bayan kisan, suna da rahotanni da ke bayani kan yadda jami’an tsaro ke tsare mutane ba tare da bari yan uwan su ko lauyoyinsu ko jami’an agaji na Red Cross sun san inda su ke ba, yayin da ya ke zargin jami’an tsaron da kona kauyuka suna sace musu dukiya.

Amurkan ta kuma zargi masu fafutukar yantar da Yankin da kashe jami’an tsaron jandarmomi da garkuwa da jami’an gwamnati da kuma kona makarantu.

Gargadin na Amurka na zuwa ne jim kadan bayan Jakada Peter Berlarin ya gana da shugaba Paul Biya a Yaounde.

An fara tashin hankalin ne a Kamaru a shekarar 2016 lokacin da masu fafutukar yancin Yankin da ake amfani da Turancin Ingilishi suka bukaci ba su yancin cin gashin kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.