Isa ga babban shafi
Iran- Turai

Turai ta kaddamar da shirin bai wa Iran kariya daga Amurka

Kungiyar Kasashen Turai ta sanar da kaddamar da shirin kare kasar Iran daga duk wani yunkuri na Amurka na kakaba ma ta takunkumi sakamakon ficewa daga yarjejeniyar nukiliyar kasar da ta yi.

Shugaban Iran Hassan Rohani
Shugaban Iran Hassan Rohani REUTERS/Stephanie Keith
Talla

Matakin na Kungiyar Kasashen Turai na zuwa ne bayan da kamfanonin kasashensu suka fara nuna shakku na ci gaba da zama a Iran sakamakon takunkumin da Amurka ta dora wa kasar wanda zai iya shafar harkokinsu na bankuna.

Bayan shugabannin kasashe 28 na Turai sun kwashe yammacin Alhamis suna tafka mahawara a tsakaninsu, shugaban gudanarwar kungiyar, Jean Claude Juncker ya ce,  juma’ar nan za su kaddamar da shirin saukakawa kamfanonin takunkumin.

Junker ya ce, matakin ya shafi gyara dokokin da za su hana tasirin takunkumin Amurka aiki a nahiyar Turai, in da yake cewa da misalin karfe 10.30 na safiyar juma’a za su yi.

Ita dai dokar ta samo assail ne a shekarar 1996, lokacin da aka kaddamar da ita domin goya wa Amurka baya kan takunkumin da ta dorawa Cuba, wadda ta hana kamfanonin Turai mu’amala da kasar.

Sabuwar dokar za ta haramta ikon duk wata kotu daga kasashen waje tasiri kan abin da ke faruwa a Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.