Yayin zanga-zangar ta jiya wadda Falasdinawan ke ci gaba da gunarwa har yau Talata, Sojin na Isra'ila sun yi amfani da makaman gurneti baya ga bindigogi da kuma hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa su tare da hallaka wasu.
Rahotanni sun ce mutane da dama ne suka fita daga hayyacinsu sakamakon hayaki mai sanya hawayen da Isra'ilan ta yini tana harbawa yankin na Gaza.
Kawo yanzu dai akwai kusan mutane 300 da suka samu mummunan rauni a zanga-zangar ta jiya, ciki har da kananan yara da shekarunsu ya gaza 12.
Tuni dai kasashen Duniya suka yi Allah wadai da matakin yayinda Majalisar Dinkin Duniya ke wani zaman gaggawa kan batun.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya ce kunnen shegun da Trump ya yi wajen bude ofishin jakadancin kasarsa a birnin na Qudus ya sanya ya rasa ikon fada ajin da kuma martabar da ya ke da ita wajen shiga tsakani don sasanta rikicin gabas ta tsakiya.
Bayan mayar da birnin na Qudus babban birnin Isra'ila hakan na nufin cewa yanzu yankin na Gaza baya da wani iko da birnin a dai dai lokacin da Isra'ilan ke ci gaba da mamaye yankin na su.