Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

Isra'ila ta hallaka Falasdinawa 59

Akalla Falasdinawa 59 Isra’ila ta hallaka ciki har da kananan yara 8 da shekarunsu bai gaza 16 ba, baya ga jikkata karin wasu fiye da dubu 2 a boren da Falasdinawan ke ci gaba da yi kan mayar da Qudus babban birnin Isra'ila.

Kasashen duniya da dama ne dai yanzu haka suka yi tir da matakin na Amurka kan ayyana kudus din a matsayin babban birnin Isra'ila wadda wasu kasashen musulmai ke kallo a matsayin haramtacciya.
Kasashen duniya da dama ne dai yanzu haka suka yi tir da matakin na Amurka kan ayyana kudus din a matsayin babban birnin Isra'ila wadda wasu kasashen musulmai ke kallo a matsayin haramtacciya. REUTERS/Mohammed Salem
Talla

Tuni dai kasashen duniya ke ci gaba da yin Allah wadai kan matakin na Amurka, wadda ta yi kunnen uwar shegu da shawarwarin da aka bata kan irin bannar da za ta haifar matukar ta ayyana Qudus din a matsayin babban birnin Isra'ila wadda yankin Falasdinu da wasu kasashen duniya ke kallo a matsayin hanaramtacciyar kasa.

Tuni dai Jagoran Falasdinawa Mahmud Abbas ya yi tir da matakin tare da ayyana zaman makokin kwanaki 3 kan mutanen da Isra'ilan ta hallaka.

Shugaban na Falasdinawa tare da takwaransa na Turkiyya Recep Tayyib Erdogan a sanarwar tir da matakin da suka fitar sun ce Amurkan ta rasa kimarta ta mai shiga tsakani a rikicin da ke faruwa a yankin gabas ta tsakiya. 

Bude Ofishin Jakandin Amurkan a birnin Kudus zai taka muhimmiyar rawa wajen karawa Isra'ila kwarin gwiwa wajen ci gaba da keta iyakokin kasashe tare da kisan gilla ga Falasdinawa masu fafutukar kwatar 'yancinsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.