Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dr. Garba Funtua kan ofishin Amurka a Kudus

Wallafawa ranar:

Yau kasar Amurka ke bude ofishinta na jakadanci a birnin Kudus duk da adawar da kasashen duniya ke yi na cewar matakin na iya dakushe shirin zaman lafiya tsakanin Israila da Falasdinu. Bude ofishin na zuwa ne a daidai lokacin da Israila ke cika shekaru 70 da kafuwa, yayin da gobe Talata ake cika shekaru 70 da kaddamar da Nakba da Falasdinawa suka yi wadda ta yi  sanadiyar raba kakaninsu sama da dubu 700 da gidajensu da kuma haifar da yaki. Akan wannan batu ne Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da  Dr. Abdulhakeem Garba Funtua, masanin siyasar Gabas ta Tsakiya.

Matakin Amurka na mayar da ofishinta daga Tel Aviv zuwa birnin Kudus ya gamu da suka daga kasashen duniya
Matakin Amurka na mayar da ofishinta daga Tel Aviv zuwa birnin Kudus ya gamu da suka daga kasashen duniya REUTERS/Amir Cohen
Sauran kashi-kashi
  • 03:16
  • 03:19
  • 03:26
  • 03:17
  • 03:40
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.