Isa ga babban shafi
Amurka-korea ta Arewa

Za a yi ganawa tsakanin Trump da Kim Jong Un a Singapore

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin takamaiman ranar da za su gana da takwaransa na Korea ta arewa Kim jong-Un bayan da ya amince da ajje shirin sa na mallakar makamin nukiliya.

Kim Jong-Un  da Shugaba Donald Trump
Kim Jong-Un da Shugaba Donald Trump SAUL LOEB / AFP / KCNA VIA KNS
Talla

A kasar Singapour ne Shugaban Amurka Donald Trump zai gana da Kim Jong Un shugaban koriya ta arewa a wani shirin kawo karshen rikicin da kasashen biyu suka tsuduma tun bayan kawo karshen yakin Koriya na shekara ta 1950 zuwa 1953.

Shugaba Trump da ya nuna yunkurin sa na ganawa da Kim Jong Un, da kan sa ne bayan tarben Amurkawa guda uku da koriya ta sako, ya bayyana cewa a wannan ganawa da Kim Jong Un ya na mai fatan za su samar da hanyoyin da za su taimaka domin kawo karshen tankiyar da ake fuskanta da kuma hakan zai taimaka domin samar da zaman lafiya mai dorewa a Duniya.

Tarihi ya nuna cewa tun bayan kawo karshen yaki Koriya kama daga shekara ta 1950 zuwa 1953 babu wani Shugaban Amurka da ya samu ganawa da wani Shugaban koriya ta arewa.

Shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un ya bayyana cewa wannan haduwa da Shugaban Amurka zai taimaka domin shihuda sabuwar halakar diflomasiya tsakanin kasashen Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.