Isra'ila ta kai wa dakarun Iran hari a Syria
Isra’ila ta kai hare-hare da makamai masu linzame a kan sansanonin sojin Iran da ke Syria, bayan da Isra’ilan ta yi zargin cewa wasu rokoki da aka kera a Iran sun fada a yankin tsaunukan Golan cikin daren jiya.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce sojin Syria sun kakkabo wasu daga cikin makaman da Isra’ila ta cilla, yayin da wasu suka fada a kusa da birnin Damascus, to sai dai babu karin bayani a game da irin asarar da wadannan hare-hare suka haifar.
Isra’ilan ta ce, kimanin rokoki 20 dakarun juyin juya halin Iran suka cilla, abin da ta bayyana a matsayin daya daga cikin manyan hare-hare da aka kaddamar mata a cikin gomman shekaru da suka gabata.
Dama dai ana ganin Isra’ila na dakon harin ramako daga Iran tun bayan da dakarun Isra’ila suka hallaka dakarun Iran bakwai a wani hari a Syria a cikin watan Afrilu.
Harin makaman rokan na zuwa bayan shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da janyewar kasarsa daga yarjejeniyar nukiliyar Iran.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu