Isa ga babban shafi
Australia

Ina so a taimaka min na mutu- Dattijo mai shekaru 104

Wani dattijo mai shekaru 104 masanin kimiyya kuma dan kasar Australia, ya bige da rera wakar da ya fi so a rayuwarsa a yayin da yake shaida wa manema labarai cewar shi dai yana so a taimaka masa ya mutu.

David Goodall mai shekaru 104 da ya zabi a kashe shi a yau Alhamis
David Goodall mai shekaru 104 da ya zabi a kashe shi a yau Alhamis REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

Bisa bayanai da suka shafi lafiyar dattijon wato David Goodall, babu wani abu da ke da alaka da tabarbarewar lafiyarsa, amma dattijon ya ce shi dai yana jin cewa, ci gaba da rayuwa a wurinshi ba shi da wani amfani.

Ya ce kwata-kwata baya bukatar rayuwa, kuma yana cike da murnar ganin zai iya samun dama a yau Alhamis ya wayi gari a barzahu.

Manema labarai da suka hada da na Rediyo da Talabijin da kuma Jaridu ne dai suka yi wa tsohon kwamba, domin samun labari.

Da aka tambaye shi ko yana bukatar wani abu mai faranta masa rayuwa? Sai dattijon ya ce, ba zai iya tunawa ba, amma ya bige da rera wata waka da yake jin dadinta.

Dattijon ya ce, ya so rayuwarsa ta fita a kasarsa wato Australia, amma ya yi bakin cikin rashin dokar bai wa mutane 'yancin zabar mutuwa, abin da ya ce, shi ya kawo shi  kasar Switzerland domin dai ya samu a kashe shi ya huta.

David ya ce, tun sa’adda ya fara tunanin yana so ya mutu, bai taba samun shakku ko tsoron a taimaka masa ya mutu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.