Isa ga babban shafi
Yemen

Mutane dubu 100 sun nemi mafaka a Yemen duk da yakin basasa

Duk da cewa kasar Yemen na fama da mummunan yakin basasa, wasu alkalumma da Hukumar Kula da Bakin Haure ta Majalisar Dinkin Duniya sun ce, akalla mutane dubu 100 ne suka yi hijira zuwa kasar domin samun mafaka.

Sama da bakin haure dubu 100 sun shiga Yemen don neman mafaka duk cewa kasar na fama da mummunan yakin basasa
Sama da bakin haure dubu 100 sun shiga Yemen don neman mafaka duk cewa kasar na fama da mummunan yakin basasa SALEH AL-OBEIDI / AFP
Talla

Hukumar ta Majalisar Duniya Duniya ta ce, a kowanne wata, akalla mutane dubu 7 ne suka rika shiga kasar ta Yemen, kuma kafin karshen shekara ta 2017 adadin bakin ya haura dubu 100.

Mafi yawan ‘yan ci-ranin sun fito ne daga kasashen yankin Kahon Afirka da ke fama da rikici, yayin da sauran bakin ba wai sun nufi kasar ta Yemen ba ne, illa kawai suna kokarin shiga yankin Gulf domin samun rayuwa tagari.

Yemen dai kasa ce da ke makotaka da Saudiya, kasar da dimbin jama’a ke shiga domin gudanar da ayyukan kwadago, duk da cewa mafi yawansu na tafiye-tafiyen ba tare da sun mallaki takardu ba.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun bayyana cewa bakin na fadawa a cikin mawuyancin hali da zarar suka isa kasar ta Yemen, musamman lura da cewa babu wata tsayayyar gwamnati ko hukuma da za ta iya ba su kariya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.