Bakonmu a Yau
Farfesa Sambo kan janyewar Amurka daga yarjejeniyar Iran
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:45
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana janye kasar daga cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran saboda abin da ya kira kura-kuran da ke ciki, yayin da ya bayyana kakaba wa kasar sabbin takunkumin karayar tattalin arziki. Tuni sauran manyan kasashen duniya suka bayyana aniyarsu ta ci gaba da mutunta wannan yarjejeniya. A game da wannan batu ne, Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Farfesa Sani Sambo, masanin harkokin siyasar duniya.