Isa ga babban shafi
Amurka

An rantsar da sabon Sakataren Wajen Amurka

An rantsar da tsohon shugaban Hukumar Leken Asirin Amurka, Mike Pompeo a matsayin sabon Sakataren Harkokin Wajen Amurka bayan da ya samu amincewar ‘yan majalisar dokokin kasar.

Sabon Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo
Sabon Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo REUTERS/Leah Millis
Talla

Tuni sabon Sakataren Wjen ya tashi daga birnin Washington domin fara ziyarar aiki a kasashen Turai da kuma Gabas ta Tsakiya.

A karshen wannan makon ne ake saran Pompeo zai isa Saudiya da Jordan da kuma Isra’ila bayan kammala taron kungiyar tsaro ta NATO yau a birnin Brussels.

Gabanin rantsar da shi, Pompeo na shiga harkokin diflomasiya domin ko a makwanni uku da suka gabata, sai da shugaba Donald Trump ya aike shi Korea ta Arewa don ganawa da Kim Jong-un gabanin taron da shugabannin kasasahen biyu za su gudanar nan gaba don tattaunawa kan batun nukiliya.

Ana kallon Mr. Pompeo a matsayin mai irin akidar shugaba Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.