Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Iran ta yi watsi da yunkurin Macron da Trump kan nukiliyarta

Rasha da Iran sun yi watsi da sanarwar da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya fitar bayan ganawarsa da Donald Trump na Amurka, da ke cewa za a sake bitar yarjejeniyar nukiliyar da kasashen duniya suka kulla da Iran a shekara ta 2015 domin sanya wasu sabbin sharudda a cikinta.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Amurka Donald Trump
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Amurka Donald Trump REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce kasar ba za ta amince da musanya yarjejeniyar wadda aka kulla kimanin shekaru uku da suka gabata ba, yana mai cewa ba hujjar da za ta sa a bukaci yin hakan.

Rouhani ya ce ko dai a ci gaba da mutunta ta kamar yadda take a yau ko kuma a’a, amma batun shiga tattaunawa domin cusa wasu sabbin batutuwa, wannan lamari ne da sam Iran ba za ta amince da shi ba.

Ita ma dai Rasha ta bakin mai magana da yawun shugaba Vladimir Putin Dimitry Peskov, ta bayyana cewa kawo yanzu ba wata mafita face ci gaba da mutunta yarjejeniyar wadda aka kulla sakamakon jajircewar kasashen duniya, in da ya ce lura da yanayin da duniya ke ciki a yau abu ne mai wuya a sake zaunawa da nufin samun irin wannan yarjejeniyar.

Kungiyar Turai wadda ta taka gagarumar rawa domin kawo karshen shirin nukiliyar kasar ta Iran, ta bakin shugabar Ofishin Kare Manufofin Ketare, Federica Mogherini, cewa ta yi duk da wancan ikirari da shugaba Macron ya yi a birnin Washington, yarjejeniyar na nan daram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.