Isa ga babban shafi
G7

Kasashen G7 na tattaunawa kan Rasha da Iran

Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Duniya 7 da suka fi karfin tattalin arziki a  sun hadu a birnin Toronto domin gudanar da taro kan yadda za su tinkari abin da suka kira tsokanar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ke yi musu. Taron zai kuma samu karin bayani akan ko shugaba Donald Trmp na Amurka zai wargaza yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran ko kuma a’a.

Ministocin Harkokin Wajen Kasashen G7 na tattaunawa kan Rasha da Iran da kuma Korea ta Arewa a Toronto
Ministocin Harkokin Wajen Kasashen G7 na tattaunawa kan Rasha da Iran da kuma Korea ta Arewa a Toronto REUTERS/Alessandro Bianchi
Talla

An dai bayyana cewar Ministocin na gudanar da taro ne domin kimtsa wa babban taron da za su yi a cikin watan Yunin wannan shekarar, amma batutuwan Rasha da Korea ta Arewa na cikin abubuwan da ke masu kaikayi.

Manyan kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a duniyar sun damu da yadda kasar Rasha ke taimaka wa shugaba Bashar al-Assad na kasar Syria a fadan da yake da ‘yan tawaye.

A ranar Litinin da ta gabata, Ministocin Harkokin Wajen Kasashen mafi karfin tattalin arzikin sun gabatar da wata sanarwa ta hadin guiwa, in da suke kira ga Rasha da ta amsa duk tambayoyin da ake mata dangane da zarge-zargen amfani da sinadarin   Novichok.

Novichok dai siddabarun hade-haden sinadarai da ke saurin hallaka dan Adam ne da gwamnatin Soviet ta samar a shekarar 1970 zuwa 1980, da gwamnatin kasar Burtaniya ta yi zargin an yi amfani da shi kan wani jami’in leken asiri a cikin watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.