Isa ga babban shafi
Saudiya

Harin dakarun hadaka na Saudiyya ya hallaka fiye da mutane 23 a Yemen

Fiye da mutane 23 suka rasa rayukansu sanadiyyar wani hari ta sama da aka kai kan wani taron aure a kasar Yemen. Harin da 'Yan tawayen Huthi ke dora alhakinsa kan dakarun sojin hadaka da ke samun goyon bayan Saudiyya. 

Hukumomin agaji a Yemen sun ce adadin mutanen da suka mutu a harin ka iya karuwa kowanne lokaci daga yanzu.
Hukumomin agaji a Yemen sun ce adadin mutanen da suka mutu a harin ka iya karuwa kowanne lokaci daga yanzu. REUTERS/FILE
Talla

Kawo yanzu dai babu tabbacin halin da ake ciki a wurin da abin ya faru, amma jami'an kiwon lafiya da kuma bangaren gwamnati na ganin adadin mutanen da suka mutu a harin ka iya karuwa.

Wasu mabanbantan rahotanni dai na nuni da cewa kawo yanzu wadanda suka jikkata ya haura 50 yayinda wadanda suka mutu kuma adadin ke tsakanin 23 zuwa 33.

A cewar kungiyoyin agaji harin ya faru ne a dai dai lokacin da ake tsaka da bikin aure a wani yanki na Bani Qais da ke lardin Hajjah, a arewacin birnin Sanaa, inda jiragen suka rika luguden wuta.

Kungiyar likitoci mai zaman kanta ta MSF, yanzu haka akwai akalla mutane 45 ciki har da kananan yara 13 da ke karbar kulawar gaggawa a wani asibiti da ke karkashin ikonta kuma dukkaninsu suna cikin mawuyacin hali.

Wananan dai shi ne hari mafi muni da dakarun na Saudiyya suka kai yankin wanda ke karkashin ikon 'yan tawayen na Houthi a baya-bayan nan, wanda kuma wani ganau ke tabbatar da cewa galibin wadanda abin ya shafa fararen hula ne.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.