Isa ga babban shafi
Faransa-Birtaniya

'Yan Majalisun Faransa da Birtaniya sun fusata kan harin Syria

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da Firaminsitar Birtaniya Theresa May sun gamu da fushin 'yan majalisun kasashensu wadanda suka nuna bacin ransu kan harin da suka kai Syria ba tare da amincewarsu ba.

'Yan majalisun Faransa da Birtaniya sun fusata da harin da Macron da May suka kai kan Syria ba tare da amincewarsu ba
'Yan majalisun Faransa da Birtaniya sun fusata da harin da Macron da May suka kai kan Syria ba tare da amincewarsu ba LIONEL BONAVENTURE / AFP
Talla

Shugabar 'yan ra’ayin rikau a Faransa, Marine Le Pen ta zargi shugaba Macron da yin gaban kansa wajen kai harin ba tare da ya nunawa 'yan majalisun kasar shaidar da yake da ita na amfani da makami mai guba ba.

Shi ma Jaen-Luc Melenchon, daya daga cikin shugabannin 'yan adawar kasar, ya yi Allah-wadai da harin, yayin da Laurent Wauquiez ya ce, bai gamsu da daukar mataki mai tsauri na kai harin ba.

A majalisar Birtaniya kuwa, shugaban marasa rinjaye Jeremy Corbyn ya bukaci sake dokar kasar wadda za ta haramta wa Firaminsita yin gaban kanta wajen kai hari ba tare da amincewar majalisar ba.

Corbyn ya ce, majalisa ce ke da hurumin karkata akalar Firaministar ba shugaban Amurka ba, saboda haka daukar mataki irin wannan ya dace ya samu amincewar 'yan majalisar.

Uwargida May ta ce, sun kai harin ne ba wai don shugaba Donald Trump ya sa su yi ba, sai don ganin dacewar yin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.