Isa ga babban shafi
Syria

Dubban 'yan Syria sun yi zanga-zangar goyon bayan Assad

Dubban 'yan kasar Syria sun gudanar da zanga-zangar nuna goyan bayan ga shugaba Bashar al-Assad a birnin Damascus, bayan harin da wasu kasashen yammacin duniya suka kai wa kasar, yayin da ake saran jami'an Hukumar Amfani da Makamai masu Guba za su isa birnin Douma a gobe Laraba don fayyace gaskiyar zargin amfani da makami mai guba kan fararen hula.

Kusan shekaru takwas kenan da ake ta gwabza yaki a Syria
Kusan shekaru takwas kenan da ake ta gwabza yaki a Syria 照片来源:路透社 REUTERS/Handout
Talla

Rahotanni sun ce, masu zanga-zangar sun yi dandazo ne a dandalin Umayyad kuma hakan na zuwa ne gabanin bikin zagayowar ranar ficewar sojojin Faransa a shekarar 1946.

Daliban makarantu sun shiga zanga-zangar dauke da tutar Syria, suna shelar cewar, "Daga Ubangiji, sai Syria, sai kuma Bashar, babu wani abu bayan haka".

Wata mata mai suna Naila Badr, ta ce, sun yi matukar farin cikin nasarar da sojojin Syria suka samu a Gabashin Ghouta.

A bangare guda, har ya zuwa jiya Litanin, kwararrun masu bincike na Hukumar Hana Amfani da Makamai masu Guba ta Duniya (OIAC) sun kasa shiga garin Duma, domin gudanar da binciken gano gaskiyar zargin da ke cewa, gwamnatin Syria ta yi amfani da makamai masu guba kan fararen hula, makwanni 2 da suka gabata, sakamakon furucin Rasha cewa, akwai matsalar tsaro a garin, in da hukumar ta sake ayyana ranar Laraba a matsayin ranar da za ta isa garin na Douma.

A wani taro da ya gudanar da mambobin kwamitin zartarwa Hukumar Hana Amfani da Makamai Masu Gubar ta Duniya 'OIAC "da ke da cibiya a birnin La Haye na kasar Hollande, shugabanta Ahmet Uzumcu, ya ce, sun kasa shiga Douma domin Rasha ta yi gargadin matsalar tsaro a garin.

Kakakin fadar Kremlin Dmitri Peskov ya karyata furucin da ke cewa, kasarsa ta ce, ana fuskantar matsalar ta tsaro da za ta hana tawagar masu binciken isa Duma, in da ya kara da cewa tun da farko Rasha ce ma ke kan gaba na son ganin an tura kwararrun masu bincike domin fayyace gaskiya ba tare da daukar bangaranci ba.

Tada jijiyoyin wuyar da ake ci gaba da yi tsakanin manyan kasashen duniya bai lafa ba duk da hare-haren maida martani da Amruka da kawayenta Faransa da Britaniya suka kai kan Syria a ranar Asabar da ta gabata, al'amarin da ka iya kara zafafa wanda kuma zai iya jefa yankin Gabas ta tsakiya a cikin mawuyacin halin barkewar yaki mai girma, in ji jakadan Rasha a Majalisar Dinikin Duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.