Amurka, Faransa da Ingila sun kaddamar da hari Syria
Shugaban Amurka Donald Trump da kansa ne ya bayar da umurni a cikin daren juma'a na soma kai farmaki a Syria, tare da hadin gwiwar kasashen Faransa da Ingila, matakin da Rasha ta danganta da rashin mutunta shugaba Vladmir Putin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A jiya juma'a ne kasar Sweden ta yada rubutacciyar matsayar da aka cimma a zauren Majalisar dinkin Duniya a kan batun aika wakilan hukumar Majalisar dinkin Duniya a Siriya don kawo karshen batun makami mai guba ga baki daya.
Bukatar aika wakilan majalisar dinkin Duniyar ta taso ne a wani taron kwamitin tsaro na majalisar dunkin Duniya.
A cikin sirri dai ne aka gudanar da taron tattaunawar kan barazanar daukar matakin Soji a kan Syria domin koya mata hankali kan zargin da ake mata na amfani da makami mai guba a yankin birnin Dhouma da ke hannun yan tawaye.
Duk da gargadin wakilan Majalisar dinkin Duniya Amurka ,Faransa da Ingila sunyi gaban kansu,lamarin da jakadan Rasha a Majalisar dinkin Duniya ya bayyana damuwa a kai tareda sanar da cewa kasar sa Rasha zata dau matakan da suka dace cikin dan karamin lokaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu