Isa ga babban shafi
Syria-Rasha

Martanin kasashen Duniya dangane da farmakin Syria

Kasashen Duniya na cigaba da mayar da martani kan hare haren da Amurka, Faransa da Birtaniya suka kaddamar a cikin Syria saboda zargin da suke mata na amfani da makami mai guba kan fararen hula.

Shugabanin kasashen Iran ,Turkiyya da Rasha
Shugabanin kasashen Iran ,Turkiyya da Rasha AFP
Talla

Gwamnatin Syria tayi Allah wadai da harin da kasashen Amurka, Faransa da Birtaniya suka kaddamar wadda suka bayyana a matsayin karan tsaye kan kasar wanda ya sabawa dokokin Duniya.

Fadar shugaban Rasha ta bayyana kiran taron kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya cikin gaggawa domin tattauna harin da tayi mummunar suka akan sa, kuma tace akwai abinda zai biyo baya.

Kasar China ta bayyana matsayin ta na kin amincewa da amfani da karfi wajen harkokin kasashen duniya, inda ta bukaci warware matsalar ta hanyar diflomasiya.

Shugaba Ayatollah Ali Khamenei na Iran ya bayyana Donald Trump da Emmanuel Macron da Theresa May a matsayin masu aikata manyan laifufuka.

Kasashen Qatar da Saudi Arabia da Turkiya duk sun bayyana goyan bayan su da kai harin, kamar yadda kungiyar NATO da Kungiyar Kasashen Turai suka yaba da matakin.

Shi kuwa Sakatare Janar na Majalisar dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci taka tsan tsan kan wannan mataki mai hadari wanda yace zai dada jefa mutanen Syria cikin halin kunci.

Kungiyar agaji ta Amnesty International ta bukaci daukar matakan kaucewa kai harin kan fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.