Isa ga babban shafi
Syria- amurka

Kasashen duniya na dari-dari kan barkewar yaki a Syria

Yayin da Amurka da kawayanta ke cewa ba gudu ba ja da baya a yunkurinsu na kai hare-hare akan kasar Syria, masu hamayya da daukar matakin soji a kan kasar karkashin jagorancin kasar Bolivia, sun bukaci Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da taron gaggawa wani lokaci yau Alhamis a asirce domin kauce wa yin fito na fiton soji tsakanin kasashen da ke da hannu a wannan rikici.A jiya Laraba shugaban Amurka Donald Trump ya ce, kowane lokaci daga yanzu za a iya daukar matakin soji a kan Syria.

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da shirin fara kaddamar da farmaki da makami mai linzami kan Syria
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da shirin fara kaddamar da farmaki da makami mai linzami kan Syria STR / RUSSIAN DEFENCE MINISTRY / AFP
Talla

Bolivia daya daga cikin kasashen da suka mara wa Rasha domin hana Kwamitin Tsaron Majalisar aikewa da masu bincike zuwa Syria, ita ce ta bukaci a sake gudanar da zaman wani lokaci a yau, lura da yadda barazanar barkewar yaki ke ci gaba da zafafa tsakanin gungun Amurka da kuma na Rasha.

Sa’o’i kadan bayan da shugaba Trump na Amurka ya sanar a shafinsa na Twitter cewa, kasar na cikin shirin kai hari da makamai masu linzame akan Syria, sakataten tsaron kasar Jim Mattis ya fito fili karara in da ya ce, dakarunsa sun shirya tsaf kuma suna jiran umurni kawai ne domin kai farmakin.

Rahotanni daga Syria dai na nuni da cewa sojin kasar da na Hezbollah sun fara canza dubarun yaki da kuma canza wa muhimman makamai wurare a barikokin sojin da ke kusa da biranen Damascus, Ghouta, Aleppo, Kuneitra, Deir Ezzor da kuma Tsaunukan Golan.

A yau Alhamis firaministar Birtaniya, wadda ke matsayin babbar kawa ga Amurka a wannan batu za ta jagoranci taron gaggawa da manyan jami’an gwamnatinta don cimma matsaya dangane da wannan batu, yayin da aka gargadi kamfanonin jiragen saman kasashen duniya da su kauce wa ratsawa sararin samaniyar yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.