Isa ga babban shafi
Brazil

Fursunoni 20 sun mutu a kokarin tserewa daga yari a Brazil

Hukumomin kasar Brazil sun ce akalla mutane 21 suka mutu lokacin da wasu yan gidan yari suka yi kokarin tserewa daga inda ake tsare da su a garin Belem da ke Jihar Para.

Wasu tarin jami'an tsaro kenan a harabar gidan yari don kaucewa yunkurin kufcewar fursunoni.
Wasu tarin jami'an tsaro kenan a harabar gidan yari don kaucewa yunkurin kufcewar fursunoni. REUTERS
Talla

Rahotanni sun ce wata kungiyar masu dauke da makamai ne suka fasa bangon gidan yarin domin kubutar da yayansu da ke ciki, abinda ya haifar da arangama tsakanin su da jami’an tsaro.

Bayanai sun ce cikin wadanda suka mutu sun hada da yan firsinan da masu kubutar da su da kuma jami’i guda.

Barazanar ballewa daga gidan yari a yankin na Latin Amurka za a iya cewa ba sabon abu bane, inda a lokuta da dama ke haddasa asarar rayuka.

Ko a watan da ya gabata ma kusan Fursunoni 70 ne suka mutu a Venezuela bayan tayar da wata gobara da gan-gan a kokarinsu na tserewa daga gidan yarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.