Isa ga babban shafi
Syria- amurka

Za mu mayar da martani mai tsauri kan harin Syria- Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi alkawarin mayar da tsattsauran martani game da zargin amfani da makami mai guba a Syria, yayin da sauran shugabannin kasashen Yammaci ke nazarin irin matakin da suka dauka.

Shugaban Amurka Donald Trump lokacin da yake jawabi kan harin makami mai guba a Douma na Syria
Shugaban Amurka Donald Trump lokacin da yake jawabi kan harin makami mai guba a Douma na Syria REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

A yayin ganawa da manema labarai, shugaba Trump ya ce, suna da zabi mai yawa ta fuskar ayyukan soji, kuma nan ba da jimawa ba za su yanke shawara kan irin martanin da za su mayar.

Mr. Trump ya ce, Amurka na samun haske kan batun wadanda ake zargi da amfani da makamin mai guba a Douma na Syria a ranar Asabar da ta gabata.

Majiyar likitoci ta bayyana cewa, gomman mutane aka hallaka a yayin kaddamar da farmakin amma kawo yanzu ba a tabbatar da takamammen adadin wadanda  suka rasa rayukansu ba.

Har ila yau, shugaba Trump ya gana da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron kan wannan harin a yammacin jiya Litinin, kuma dukkaninsu sun bayyana aniyarsu ta daukan martani mai tsauri kamar yadda fadar Elysee ta sanar.

Ita ma Firaministar Birtaniya, Theresa Ma ta yi Allah-wadai da harin, in da ta bukaci a tuhumi masu mara wa shugaba Bashar al-Assad baya.

Wannan dai na zuwa ne bayan Kwanmitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zama kan batun a jiya, in da Amurka da Rasha suka yi musayar zafafan kalamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.