Isa ga babban shafi
Indonesia

Barasa ta kashe mutane 90 a Indonesia

Sama da mutane 90 ne suka mutu, a yayin da wasu gommai ke can kwance a assibiti sakamakon shan wata giyar da aka sarrafa ta a gida a Indonesia.

Gwamnatin Indonesia ta sanya haraji mai yawan gaske don hana shigo da giya daga kasashen ketare
Gwamnatin Indonesia ta sanya haraji mai yawan gaske don hana shigo da giya daga kasashen ketare AFP PHOTO/FARZIN NEMATI
Talla

Yanzu haka dai, jami’an tsaro na kai samamen cafke duk masu sayar da wannan barasar tare da zakulo masu sarrafat  a fakaice, musamman a manyan biranen kasar ta Indonesia.

Dama dai Indonesia kasa ce ta Musulmai, kuma sarrafa giyar da kuma shanta duk haram ne a hukumance, abin da ya sa hukumomin kasar suka lankaya wa masu shigar da ita daga wasu kasashen haraji mai yawan gaske da nufin kawar da shigar da ita cikin kasar.

Ko a shekarar 2016, sai da aka asarar rayuka 36 sakamakon shan gurbatacciyar barasar.

Yanzu haka dai hukumomin kasar sun  damke mutane 7 da ake tuhuma da ko dai sarrafawa ko kuma sayarwa ko kuma dai kwankwadar barasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.