Isa ga babban shafi
Saudiya-Faransa

Yarima Salman na Saudiya na ziyara a Faransa

Yarima mai jiran gado na Saudiya, Mohammed Salman, ya isa Faransa don fara gudanar da ran-gadinsa karo na biyu a kasashen duniya da zimmar kawo sauyi a kasarsa da ake danganta ta da tsattsauriyar akida.

Ana saran Yarima Salman na Saudiya zai kulla yarjeniyoyin Dala a Faransa
Ana saran Yarima Salman na Saudiya zai kulla yarjeniyoyin Dala a Faransa ©BANDAR AL-JALOUD/Saudi Royal Palace/AFP
Talla

A yayin ziyarar ta kwanaki biyu, yarima Salman na Saudiya zai gana da shugaban Faransa, Emmanuel Macron kuma karon farko kenan da ya ziyarci kasar a matsayinsa na mai jiran gadon mulkin Saudiya.

A tattaunawar da za su yi, Salman da Macron za su mayar da hankali kan huldarsu ta al’adun gargajiya da zuba hannayen jari har ma da yakin da ake fama da shi a Yemen baya ga batun da ya shafi Iran da ta kasance mai takun saka da Saudiya.

Wata majiya mai kusanci da tawagar yariman na Salman, ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Farana na AFP cewa, bangarorin biyu za su sanya hannu kan wasu yarjeniyoyin fahimtar juna 18 da suka danganci makamashi da ayyukan gona da yawon bude ido da al’addun gargajiya a wani zaman taro da za su yi a gobe Talata.

Baya ga ganawarsa da Macron da Firaministan Faransa da kuma hukumomin kasuwancin kasar, har ila yau yariman zai ziyarci wani sansanin habbaka fasaha da ke birnin Paris da kuma cibiyar Larabawa ta Duniya.

Ziyarar Salman na zuwa ne bayan makamanciyarta da ya kai kasashen Amurka da Birtaniya da Masar, in da ya gana da attajiran ‘yan kasuwa tare da kulla yarjeniyoyin miliyoyin Dala a bangaren tsaro da nishadantarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.