Isa ga babban shafi
Faransa-Mali

Sojin Faransa da Mali sun kashe 'yan ta'adda 30

Dakarun sojin Faransa da Mali sun kashe mayakan jihadi 30 a wani dauki-ba-dadi da suka yi da su a kusa da kan iyakar Mali da Nijar.

Sojin Faransa da na Mali sun kashe mayakan jihadi 30 a kan iyakar Mali da Nijar
Sojin Faransa da na Mali sun kashe mayakan jihadi 30 a kan iyakar Mali da Nijar AFP / A. Abdulle Abikar
Talla

Mai magana da yawun rundunar sojin Faransa, Kanar Patrick Steiger ya ce, an yi dauki ba dadin ne a ranar Asabar da ta gabata a yankin Akabar da mayakan jihadi kimanin 60, yayin da ya ce, dakarun Mali sun yi asara a fafatawar, amma babu abin da ya samu na Faransa.

Tun a ranar 28 ga watan Maris ne kwamandojin sojin Faransa da Mali suka fara sanya ido a yankin Akabar, in da suke aikin hadin gwiwa da takwarorinsu na Nijar da kuma wata kungiyar sa kai.

‘Yan ta’adda dai sun yi kaka-gida a kan iyakar da ke yankin na Akabar.

Kasar Faransa dai ta aike da jiragen sama masu saukar ungulu biyu da kuma wasu jiragen yaki biyu don taimaka wa dakarun da ke yankin, amma kawo yanzu ba a yi amfani da wadannan jirage wajen kai hare-hare ba kamar yadda mai Magana da yawun rundunar ya sanar.

Tun dai a cikin shekarar 2013 ne Faransa ta shiga Mali don taimaka wa kasar fatattakar mayakan jihadin da ke da alaka da kungiyar al-Qaeda a arewacin kasar.

Sai dai ayyukan ta’addancin sun yadu har zuwa tsakiya daa kudancin Mali tare kuma da kwararar mayaka cikin Burkina Faso da Nijar, lamarin da ya sa aka kafa runduna ta musamman don yaki da ‘yan ta’adda a kasashen yankin Sahel da suka hada da Chadi da Mauritania.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.