Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka

Korarrun jakadun Rasha daga Amurka sun isa gida

Jami’an Diplomasiyyar Rashan nan da Amurka ta kora a makon jiya sun isa gida, a dai dai lokacin da mahukuntan Moscow ke gargadin 'yan kasar game da balaguro zuwa Birtaniya, abin da ke dada fito da tsamin dangantaka tsakanin kasashen biyu  biyo bayan harin gubar da ake zargin Rasha da kai wa cikin Birtaniya.

Jakadun Rasha da Amurka ta sallama sun isa gida
Jakadun Rasha da Amurka ta sallama sun isa gida REUTERS/Chris Radburn
Talla

Wannan dai shi ne yakin cacar baka mafi tsami da aka taba gani a tarihi, wanda cikin kankanin lokacin ake ganin matakan martanin gaggawa a diplomasiyyance tsakanin Rasha da kasashen Yamma.

Wani abu da ke kara tsamin danganta kuwa shi ne yadda Rashan ta sanar da 'yan kasar ta cewa, su kaurace wa tattaki zuwa Birtaniya don kauce wa cin zarafi ko tsangwama.

Birtaniya dai na ci gaba da hakikancewa Rasha ce ke da alhakin kai harin gubar kan Sergie Skripal, tsohon jami’in leken asirinta da ke aiki da Birtaniya, zargin da Rasha ta sha musantawa.

Tuni dai wani jirgin sama dauke da mutane 170, wato iyalan jami’an da Amurka ta kora ya sauka a birnin Moscow.

A jumulce dai jami’an Rashan kusan 150 ne kasashen duniya suka sallama a wani mataki na mara wa Birtaniya baya kan abin da take zargin Rashan da aikatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.