Isa ga babban shafi
Falasdinu

Kananan yara na cikin hatsari a Gaza- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, matukar aka gaza daukan matakan gaggawa, to babu shakka rayuwar kananan yara a Zirin Gaza zai fada cikin hadari a dai dai lokacin da  Falasdinawa za su gudanar da wani gangami a kan iyakar Gaza da Isra’ila, abin da ake ganin zai haifar da tashin hankali tsakanin bangarorin biyu.

Akwai kananan yara da dama a yankin Gaza
Akwai kananan yara da dama a yankin Gaza REUTERS/Mohammed Salem
Talla

A cewar Jakadan Majalisar Dinkin Duniyar a Gabas ta Tsakiya, Nicloy Mladinov, ya kamata kowanne bangare ya sassauta don gudun barkewar rikici tsakanin Falasdinawa da Yahudawa a yayin gangamin.

Yanzu haka dai dandazon iyalan Falasdinawa ne ke shirin kafa daruruwan tantuna a wani wuri da ke iyakar Gaza da Isra’ila, a wani mataki na kaddamar da makon nuna goyon baya ga Falasdinawa ‘yan gudun hijira.

Sai dai Jakadan ya ce, abin fargabar shi ne yadda makomar kananan yara za ta kasance a lokutan rikicin.

Gangamin dai na cikin bikin tunawa da kisan wasu Larabawa shida wadanda ba su dauke da makamai a shekarar 1976, lokacin wani bore a Isra’ila.

Sai dai a ranar 15 ga watan Mayu ne Falasdinawan ke saran kawo karshen gangamin, wanda kuma yaci karo da bikin cikar Isra’ila shekaru 70 da kafuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.