Isa ga babban shafi
Faransa

Ma'aikata sun yi gagarumar zanga-zanga a Faransa

Ma’aikatan gwamnatin Faransa sun gudanar da gagarumar zanga-zangar gargadi ga shirin shugaba Eammanuel Macron na samar da sauye-sauye a fannoni da dama. An dai soke zirga-zirgar jiragen kasa da na sama sakamakon zanga-zangar a sassan kasar, abin da ya jefa dubban mutane cikin kunci.

Dandazon masu zanga-zangar adawa da shirin shugaba Emmanuel Macron a Faransa
Dandazon masu zanga-zangar adawa da shirin shugaba Emmanuel Macron a Faransa REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

An dai rufe makarantu da cibiyoyin renon kananan yara har ma da dakunan karatu gabanin gagarumar zanga-znagar a sassan Faransa , yayin da ayyukan wasu hukumomi ya gamu da cikas kamar masu aikin karbar shara a Paris da sauran birane.

Daya daga cikin shugabannin kungiyoyin kwadago a kasar, Jean Claude Maily ya ce, akwai bukatar gwamnati ta mayar da hankali sosa kan wahalhalun da ma’aikata ke fuskanta.

Zanga-zangar ta baya-bayan nan na a matsayin zakarar gwajin dafi kan karfin shugaba Emmanuel Macron da ke gaban kansa wajen aiwatar da manufofinsa na sauye-sauye a fannin jiragen kasa da sauran ma’aikatun gwanmati.

Ko a cikin watan Oktoban da ya gabata, dubban mutane sun gudanar da zanga-zangar adawa da shirin Macron na rage ma’aikata dubu 120 a cikin wa’adinsa na shekaru biyar.

A can baya dai kungiyoyin kwadago a Faransa sun sha tilasta wa gwamnati dakatar da daukan wasu matakai, amma a wannan karo shugaba Macron da ministocinsa sun ce ba gudu ba ja da baya.

An kiyasta cewa, kusan mutane dubu 50 ne suka shiga zanga-zangar ta yau a birnin Paris kadai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.