Birtaniya, kasashen Turai ba sa adawa da takarar Buhari a 2019
Kasar Birtaniya ta ce, ba ta adawa da takarar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na neman wa’adi na biyu a zaben kasar na shekara mai zuwa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Jakadan Birtaniya a Najeriya, Paul Arkwright ya shaida wa jaridar Premium Times cewa, Birtaniya da daukacin kasashen Yammacin duniya ba sa adawa da takarar shugaban na Najeriya.
Arkwright ya yi watsi da zargin cewa, kasashen Yammacin duniya ba sa tare da shugaban Najeriya kan shirin takarar neman wa’adi na biyu, in da yake cewa 'yan Najeriya ne ke da hurumin yanke hukunci kan takarar ta shi.
Ya zuwa yanzu shugaban Najeriya Muhammadu Buhari bai fito karara ya bayyana shirin yin takara a zaben shekara mai zuwa ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu