Isa ga babban shafi
Rahoto

Mata miliyan 56 na fuskantar hadari a zabur da ciki

Wani binciken masana ya bayyana cewar sama da zubar da ciki miliyan 56 da ake yi kowccee shekara a duniya na tattare da hadari, abin da ke kai ga rasa rayukan akalla dubu 22da 800.

Akwai mata da dama da ke rajin kare halascin zubar da ciki a sassan duniya
Akwai mata da dama da ke rajin kare halascin zubar da ciki a sassan duniya Reuters/Clodagh Kilcoyne
Talla

Cibiyar Guttmacher da ta gudanar da binciken akan zub da ciki a kasashen duniya, ta ce,haramta zubar da cikin bai hana mata zubar da shi ba, sai dai ya kan kara jefa su cikin hadari.

Cibiyar ta ce, yayin da aka samu raguwar masu zubar da cikin a kasashen da suka ci gaba shekaru 25 da suka gabata, matsalar ta karu a kasashe masu tasowa.

Rahotan ya bayyana kasashen da suka saukaka dokar zubar da ciki 33 tsakanin shekara ta 2000 zuwa 2017 da suka hada da Nepal da Uruguay da Nijar da Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.