Isa ga babban shafi
EU-US

EU za ta fara karbar haraji mai yawa daga kamfanonin Amurka

Kungiyar Tarayyar Turai ta kaddamar da kudirin dokar sanya harajin yanar gizo kan manyan kamfafonin fasaha na Amurka da suka hada da Facebook da ke cikin tsaka mai wuya sakamakon zargin sa da tatsar bayanan mutane miliyan 50, lamarin da ya girgiza duniya.

Facebook na cikin manyan kamfanonin Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai ke shirin maka wa haraji
Facebook na cikin manyan kamfanonin Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai ke shirin maka wa haraji REUTERS/Yves Herman/Foto Archivo
Talla

Matakin sanyan harajin na musamman shi ne na baya-bayan nan da gungun kasashen Turai 28 ya kaddamar kan manyan kamfanonin fasaha na Amurka da ke yankin Silicon Valley.

Sai dai ana ganin wannan mataki ka iya zafafa dacin sabanin huldar kasuwanci tsakanin kasashen Tarayyar Turai da shugaban Amurka Donald Trump.

Kwamishinan Harkokin Kasuwanci na Kungiyar Kasashen Turai, Pierre Moscovici ya kaddamar da kudirin ne a birnin Brussels da zimmar tara biliyoyin kudi na Euro daga kamfanonin Amurka da suka karkata akalarsu ta neman kudin shiga a kasashen Turai saboda saukin biyan haraji.

Kwamishinan ya ce, dokar sassaucin karbar kudin harajin na haddasa matsananicn karancin kuadaden shigar gwamnati a kasashen na Turaai.

A cewar Kwamishinan matukar aka sanya harajin da kashi uku akan manyan kamfanoni, to babu shakka hakan zai bada damar samun kudaden da suka kai Euro biliyan biyar a shekara guda.

Kamfanonin da matakin zai shafa sun hada da Facebook da google da Apple da kuma Amazon da suka shahara ta fannin harkokin yanar gizo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.