Isa ga babban shafi
Syria

Sojin Syria sun kwace iko da yankunan 'yan tawaye 2

Sojin Syria sun kwace iko da wasu yankuna biyu daga hannun 'yan tawayen kasar da ke wajen birnin Damascus a yammacin yau Asabar bayan wasu jerin hare-hare da luguden wuta ta sama da suka tilastawa daruruwan fararen hula tserewa daga yankin.

Wasu fararen hula kenan da ke neman mafaka don tsira da rayukansu bayan wasu hare-haren bama-bamai ta sama da sojin Syria suka kaddamar a yankunan gabashin Damascus yau Asabar.
Wasu fararen hula kenan da ke neman mafaka don tsira da rayukansu bayan wasu hare-haren bama-bamai ta sama da sojin Syria suka kaddamar a yankunan gabashin Damascus yau Asabar. Abdulmonam Eassa/AFP
Talla

Sojin Syria bisa taimakon sojin kawancen kasashen Rasha sun kwace yankunan Kafr Batna da Sabqa daga hannun 'yan tawayen a dai dai lokacin da dubban fararen hula ke ci gaba da ficewa daga kasar don tsira da rayukansu.

Kawo yanzu dai gwamnatin Syria na rike da kimanin kashi 80 cikin dari na yankunan da ke hannun 'yan tawayen a bayatun bayan luguden wutar da ta kaddamar a ranar 18 ga watan  Fabarairun da ya gabata.

Masu sanya idanu kan rikicin na Syria sun ce 'yan tawayen gwamnatin yanzu sun kasu zuwa gida uku yayinda kowanne ke ikirarin iko da wani bangare a yankunan da suka rage a hannunsu.

Daga cikin bangarorin 'yan tawayen a cewar hukumar kare hakkin dan adam ta Birtaniya da ke sanya ido kan rikicin na Syria, akwai 'yan tawayen Faylaq al-Rehman da Jaish al-Islam da kuma Ahrar al-Sham wadanda ke da mayaka fiye da dubu 8, sai dai dukkaninsu bayan luguden wutar na yau sun dawo basa iko da komi face wasu tsiraran yankuna.

Kawo yanzu dai adadin farern hular da suka mutu tun bayan fara luguden wutar a cikin kasa da watanni biyu sun kai fiye da Mutane dubu daya da dari hudu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.