Isa ga babban shafi
Afghanistan

Taliban na shirin tattaunawar sulhu da Afghanistan

Jiga-jigan Kungiyar Taliban sun bayyana aniyarsu ta shiga tattaunawa da gwamnatin Afghanistan kamar yadda Sakataren Tsaron Amurka, Jim Mattis ya sanar a ziyarar ba-zata da ya kai birnin Kabul a yau Talata.

Sakataren Tsaron Amurka Jim Mattis a birnin Kabul na Afghanistan
Sakataren Tsaron Amurka Jim Mattis a birnin Kabul na Afghanistan Reuters
Talla

Ziyarar Sakataren Tsaron Amurka, Jim Mattis a Kabul na zuwa makwanni biyu da shugaban Afghanistan , Ashraf Ghani ya sanar da shirin shiga tattaunawar zaman lafiya da Taliban da ta kasance babbar kungiyar ‘yan tawaye a kasar.

Kawo yanzu dai, mayakan kungiyar ba su amsa tayin gwamnatin kasar ba na shiga tattaunawar a hukumance ba, amma a cewar Mr. Mattis wasu daga cikin jagororin kungiyar sun nuna sha’awarsu ta zaman sulhun.

Mattis ya ce, ko da dai mawuyaci ne dukkanin mambobin Taliban su amince da wannan batu lokaci guda, amma babu shakka akwai manyansu da suka bayyana aniyarsu karara ta tattaunawa da gwamnatin Afghanistan.

Daga cikin tsarin shugaba Ashraf Ghani na tattaunawar zaman lafiyar, akwai batun amincewa da kungiyar Taliban a matsayin jam’iyyar siyasa a kasar .

Taliban ta ce, a shirye take ta yi zaman sulhun amma tare da gwamnatin Amurka, abin da ya sa Mattis ya bukaci mahukuntan Afghanistan da su tanadar da matakan sulhun.

A makon jiya ne, Taliban ta bayyana gwamnatin Afghanistan a matsayin haramtacciya, tare da fadin cewa, tsarinta na zaman sulhun na cike da yaudara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.