Isa ga babban shafi
Syria

Amurka ta bukaci sabon tsagaita wutar kwanaki 30 a Syria

Amurka ta shigar da wani sabon kudiri ga zaman Majalisar Dinkin Duniya da ke neman tsagaita wuta na kwanaki 30 a yankin Gabashin Ghouta da gwamnati ke luguden wuta akansa. Jakadiyar Amurka a zauren Majalisar Nikky Haley ta shaidawa kwamitin tsaro na Majalisar cewa tsagaita wutar da ya bukata a baya bayyi tasiri ba.

Jakadiyar Amurkan ta ce ko bayan  da Rashan ta amince da tsagaita wutar sai da ta kai wasu farmakai na bama-bamai har sau 20 a biranen Damascus da Ghouta
Jakadiyar Amurkan ta ce ko bayan da Rashan ta amince da tsagaita wutar sai da ta kai wasu farmakai na bama-bamai har sau 20 a biranen Damascus da Ghouta REUTERS/Eduardo Munoz
Talla

A cewar Nikky Haley tsagaita wutar da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar ya bukata a baya ya gaza yin aiki don samun damar shigar da kayakin agaji ga dubban fararen hular da ke bukatar agajin abinci da magunguna, sakamakon yadda Syria bisa goyon bayan Rasha suka ki mutunta yarjejeniyar tare da ci gaba da luguden wuta a yankin na gabashin Ghouta.

Haley ta ce yanzu za su gabatar da wata sabuwar bukatar tsagaita wutar ta yadda babu yadda za a yi wasu su yi mata hawan kawara, inda ta zargi Rasha da rashin mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar duk da cewa ta kada kuri’ar amincewa da hakan a gaban majalisar dinkin duniyar.

Jakadiyar Amurkan ta ce ko bayan da Rashan ta amince da tsagaita wutar sai da ta kai wasu farmakai na bama-bamai har sau 20 a biranen Damascus da Ghouta.

Haley ta kuma bukaci majalisar ta gaggauta daukar mataki kan duk wata kasa da ta yi yunkurin wargaza tsagaita wutar dama duk wata kasa da ta kai hare-hare da makamai masu guba kan al’umma a Syrian.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.