Isa ga babban shafi
Faransa- Amurka

Faransa ta goyi bayan daukan mataki kan Amurka

Gwamnatin Faransa ta goyi bayan shirin Kungiyar Tarayyar Turai na mayar da martani kan matakin shugaban Amurka Donald Trump na tsawwala haraji kan kayan karafa da goran-ruwa wato Alminium da ake shiga da su Amurka.

Shugaba Donald Trump na dab da sanya hannu kan dokar tsawwala harajin kafara da goran-ruwa da ake shigowa da su Amurka
Shugaba Donald Trump na dab da sanya hannu kan dokar tsawwala harajin kafara da goran-ruwa da ake shigowa da su Amurka REUTERS/Chris Keane
Talla

Acewar Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean Yves Le Drien, dole ne Tarayyar Turai ta kare martabarta don nunawa shugaba Trump iyakarsa tare kuma da kara fayyace ma sa cewar, kasar ce za ta ji jiki a wannan lamari.

Le Drien ya kara da cewa, martanin gaggawa shi ne abin da yafi dacewa a irin wannan yanayi.

Shi ma a nasa bangaren Kwamishinan Tarayyar Turai, Pierre Mascovici cewa ya yi matakin dakatar da shigar da kayan Amurka zuwa Turai ya zama wajibi idan har Trump ya sanya wa dokar hannu, kuma in ji shi matakan za su shafi kamfanonin manyan jami'an gwamnatin Trump da ma shugaban Majalisar Dokoki, Paul Ryan.

Sauran kayayyakin sun hada da lemuka da taba sigari da alawoyin chakulan, baya ga kuma manyan kayayyaki da suka hada da motoci da babura kamar yadda shugaban Tarayyar Turan Jean Claude  Juncker ya bayyana.

Ana dai ganin matakin na Trump na da babbar barazana ga dubban ayyukan yi a nahiyar Turai, abin da ya sa kenan Tarayyar Turan ke daukar matakan kariya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.