Isa ga babban shafi
Italiya

Haifaffen Gusau ya lashe kujerar sanata a Italiya

Wani haifaffen birnin Gusau da ke jihar Zamfara a Najeriya amma mazaunin Italiya, ya yi nasarar lashe kujerar sanata a Majalisar Dattawan kasar, in da ya zama mutun na farko bakar fata da aka zaba akan wannan mukami a duk fadin kasar duk da cewa ya tsaya ne a karkashin jam’iyya mai kyamar baki.

Toni Iwobi ya shafe kimanin shekaru 40 a Italiya
Toni Iwobi ya shafe kimanin shekaru 40 a Italiya ndtv.com
Talla

Toni Iwobi ya lashe zaben ne a karkashin jami'yyar League Party mai adawa da kwararar baki a mazabar Brescia da ke arewacin Italiya.

An haifi Iwobi a garin Gusau da ke jihar Zamfara amma tun a tsakan-kanin shekarar 1970 ya ke zaune a Italiya.

Jim kadan da zabensa, Mr. Iwobi ya aike da sakon murna a shafinsa na Facebook, in da ya ce, ana dab da ganin sauyi.

Iwobi ya shafe sama da shekaru 20 a matsayin mai goyon bayan jam’iyyar League Party mai ra’ayin rikau , in da ya shiga sahun masu yaki da kwararar bakin haure dubu 690 daga yankin arewacin Afrika.

Sabon Sanatan ya ce, kwararar bakin haure cikin Italiya ba bisa ka’ida ba na tsananta matslar wariyar launin fata a kasar.

Mr. Iwobi ya shiga Italiya a matsayin dalibi kimanin shekaru 40 da suka gabata, in da ya auri baturiyar kasar kafin daga bisani ya bude kamfanin fasahar sadarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.