Isa ga babban shafi
Korea ta Kudu

Tawagar Korea ta Kudu na ganawa da Kim Jong Un na Arewa

Manyan jami’an gwamnatin Korea ta Kudu sun isa birnin Pyongyang na Korea ta Arewa don ganawa da shugaba Kim Jong Un.Tawagar Jami’an za ta yi amfani da ganawar wajen share fagen tattaunawa tsakanin Amurka da Korea ta Arewa mai takama da karfin makamin Nukiliya

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un na takun saka da Amurka saboda gwajin makamin nukiliya
Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un na takun saka da Amurka saboda gwajin makamin nukiliya REUTERS
Talla

A karon farko kenan cikin sama da shekaru 10 da wata tawagar manyan jami’an gwamnatin Korea ta Kudu ke ziyartar Korea ta Arewa, matakin da ke a matsayin yunkurin baya-bayan nan na ci gaba da inganta hulda tsakanin kasashen biyu tun bayan da Korea ta Arewa ta aike da ‘yan wasanta Korea ta Kudu don halartar gasar Olympics ta kakar hunturu.

Tawagar za ta yi kokarin samar da kafar tattaunawa tsakanin Amurka da Korea ta Arewa da ke takun saka da juna bayan Korea ta Arewa ta yi barazanar kai wa Amurka farmaki.

Shugaban Korea ta Kudu, Moon Jae-in ya bukaci amfani da wasannin Olympics din da kasarsa ta karbi bakwanci wajen sasantawa tsakanin mahukuntan Washington da Pyongyang don ganin sun kai zuciya nesa a barazanar harbe-harben makamin Nukiliya.

Mai bai wa shugaba Jae-in shawara kan harkokin tsaro Chung Eui-yong ya ce, babu shakka akwai kalubale a wannan yunkuri na sasantawa, la’akari da cewa Korea ta Arewa ta yi watsi da takunkuman da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba ma ta saboda gwaje-gwajenta na makamin Nukiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.