Mu Zagaya Duniya
Halin da ake ciki a kasar Burkina Faso bayan kai hare-haren ta'addanci a birnin Ouagadugou
Wallafawa ranar:
Kunna - 20:07
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon, kamar yadda aka saba ya yi bitar wasu daga cikin manyan labarun da suka faru ne a duniya. Daga cikin manyan labaran duniyar da shirin ya tabo akwai taron farfado da tafkin Chadi, halin da ake ciki dangane da kokarin ceto daliban makarantar Dapchi da mayakan Boko Haram suka sace, da kuma harin ta'addancin da aka kai a babban birnin kasar Burkina Faso, Ouagadugou.