Jamus da Faransa sun bukaci matsin lamba kan Syria
Shugabannin Jamus da Faransa sun bukaci Rasha da ta tsananta matsin lamba kan gwamnatin Syria don ganin ta aiwatar da yarjejeniyar tsagaita musayar wuta ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar.Wannan na zuwa ne bayan dakarun kasar sun sake kaddamar da sabon farmaki kan fararen hula a yankin Ghouta.
Wallafawa ranar:
Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel da takwaranta na Farasa, Emmanuel Macron sun tattauna da shugaba Putin na Rasha ta wayar tarho, in da suka jaddama masa muhimmancin gaggauta aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Syria mai fama da rikici.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin gwamnatin Jamus ta ce, Uwargida Merkel da Macron da Putin duk sun yi madalla da yarjejeniyar tsagaita musayar wuta ta kwanaki 30, musamman don bada damar shigar da kayayyakin agaji tare da kwashe fararen hula daga yankin da yaki ya kazanta.
Shugabannin sun gana ne bayan Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci cimma yarjejeniyar ta kwanaki 30 a Syria a ranar Asabar.
Sai dai bayan wannan zama, dakarun gwamnatin Syria sun sake kai farmaki a Ghouta tare da kashe fararen 41 kamar yadda kungiyar da ke sa ido a Syria mai cibiya a Birtaniya ta sanar.
Sama da fararen 500 ne ake zaton sun rasa rayukansu a cikin mako guda sakamakon barin wutar da dakarun gwamnatin Syria suka yi a yankin gabashin Ghouta da ke kusa da birin Damascus.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu