Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 22/02 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 22/02 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 22/02 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 22/02 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 22/02 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 22/02 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 22/02 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 22/02 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/02 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/02 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 22/02 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Duniya

Amurka ta tsayar da ranar mayar da Ofishinta birnin Qudus

media 美国总统特朗普与地方官员会面。2018-02-22 Tun bayan wancan mataki na Trump ne Mahmud Abbas ke ci gaba da neman amincewar manyan kasashen Duniya da kuma majalisar dinkin duniya wajen ganin sun mara baya ga zamowar Palasdinu kasa mai cin gashin kanta. 路透社。

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce kasar za ta kammala mayar da Ofishin jakadancinta na Isra'ila zuwa birnin Kudus a cikin watan Mayun shekarar nan, dai dai da lokacin da Isra'ilan za ta yi bikin cikarta shekaru 70 da kafuwa.

 

Tuni dai shugabannin Falasdinawa suka yi tir da matakin tare da bayyana shi a matsayin babbar barazana ga zaman lafiyar yankin Larabawa.

Kafin yanzu dai Amurkar ta sanar da shekarar 2019 a matsayin lokacin da za ta yi aikin mayar da ofishin na ta birnin Qudus sai dai kuma sauyawar a cewar shugabannin Falasdinawa baya rasa nasaba da kokarin da Jagoran Falasdinawan Mahmud Abbas ke ci gaba da yi na ganin duniya ta amince da Falasdinu a matsayin kasa.

A watan Disamban bara ne dai shugaban Amurka Donald Trump ya yi kunnen kashi tare da ayyana birnin na Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila maimakon Tel Aviv, duk kuwa da kin amincewar manyan kasashen duniya dama majalisar dinkin duniya.

Ko da yake dai Trump din ya ce matakin baya da nufin haddasa rikici tsakanin bangarorin biyu masu gaba da juna, sai dai kuma a zahiri batun na da nasaba da kara tunzura Falasdinawa a dai dai lokacin da Isra'ilan ke ci gaba da mamaye musu yankuna.

Tun bayan wancan mataki na Trump ne Mahmud Abbas ke ci gaba da neman amincewar manyan kasashen Duniya da kuma majalisar dinkin duniya wajen ganin sun mara baya ga zamowar Palasdinu kasa mai cin gashin kanta.

Ko a ranar Talatar makon nan ma, Mahmud Abbas yayin jawabinsa gaban Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci samarwa da Falasdinu kujerar din-din-din a majalisar, yayinda a bangare guda kuma ya nemi gudanar da wata tattaunawar sulhu da za ta kai ga kafa kasar Falasdinu.

 

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure