Isa ga babban shafi
Syria

Rasa rayukan fararen hula a Syria abin tada hankali ne - Guterres

Kasashen Duniya na ci gaba da matsin lamba ga gwamnatin Syria kan ta kawo karshen munanan hare-haren da ta ke kai wa kan fararen hula a yankin Ghouta wanda yanzu haka yayi sanadin hallaka fararen hula sama da 300.

Wani karamin yaro zaune a gaban wasu gine-gine da hare-haren jiragen yaki suka rusa a yankin Arbin da ke gaf da birnin Damaskas.
Wani karamin yaro zaune a gaban wasu gine-gine da hare-haren jiragen yaki suka rusa a yankin Arbin da ke gaf da birnin Damaskas. REUTERS/Bassam Khabieh
Talla

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana kashe-kashe a matsayin abin tada hankali wanda yayi kama da wutar Jahannama a doron kasa.

Shi kuwa shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya bukaci tsagaita wuta cikin gaggawa domin gudanar da ayyukan jinkai a yankin na gabashin Ghouta.

Yau ake saran kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri’ar amincewa da tsagaita wutar kwanaki 30 domin kai kayan agaji ga mazauna yankin.

Rahotanni sun ce akasarin asibitocin yankin sun rushe sakamakon hare haren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.