Isa ga babban shafi
Syria

Dakarun Syria sun sake kashe mutane a Ghouta

Sojin gwamnatin Syria sun sake kaddamar da jerin munanan hare-hare kan 'yan tawayen da ke gabashin lardin Ghouta tare da hallaka mutane kusan 20. Cikin kwanaki biyar kacal, hare-haren dakarun sun hallaka mutane 360 tare da jikkata kusan  dubu 2.

Mutane 360 sun mutu cikin kwanaki biyar a hare-haren Ghouta
Mutane 360 sun mutu cikin kwanaki biyar a hare-haren Ghouta REUTERS/ Bassam Khabieh
Talla

Yanayin dai ya munana matuka cikin kwanaki biyar din da sojin gwamnatin kasar suka yi na luguden wuta babu kakkautawa a Ghouta, abin da ya hallaka daruruwan fararen hula, wanda galibinsu kananan yara ne da mata.

Rasha ta ce, ta shaida wa dakarunta da su umarci mayakan su fice cikin lumana daga yankin, rokon da ta ce mayakan sun yi watsi da shi, in da suke ci gaba da amfani da fararen hula a matsayin garkuwa.

Masu sanya ido game da rikicin sun ce, akwai tarin sojojin da suka ja daga kuma suke shirin shiga lardin ta kasa.

Tuni dai Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi kiran gaggata dakatar da farmakin, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce, ko kadan babu hannun kasar cikin wannan rashin imanin da ke faruwa a Ghouta.

Haka ita ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wadda ta bayyana lamarin da kisan kare dangi, ta kuma zargi Bashar al Asaad da kisan jama’ar kasarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.